1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fargabar barkewar sabon rikici a Burundi

Bisa ga alamu kurar rikicin Burundi ta lafa, amma masana na gargadi game da yiwuwar barkewar sabon rikici a kasar musamman dangane da halin da ake ciki.

Tun a cikin wata Afrilu na shekarar 2015 Burundi ta fada cikin wani rikici na siyasa wanda ya rikide ya koma tashin hankali bayan da shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar. Matakin da ya bashi damar yin wa'adi na uku na mulki duk kuwa da cewar doka ta haramta hakan. Wannan kuwa ya janyo mummunar zanga-zanga ta 'yan adawa a kasar wadanda sau tari jami'an tsaro ke bude musu wuta a lokacin boren.

Akalla mutane 400 suka rasa rayukansu a sakamakon tashin hankali yayin da wasu dubu 250 suka fice daga matsugunansu zuwa kasashen ketare domin yin hijira bayan da aka sake zaben Nkurunziza a kan karagar mulki a cikin watan Yulin 2015.

Tun farko gwamnatin ta Burundi ta girka wani kwamiti wanda ke kula da sake sasanta tsakanin 'yan siyasar kasar, amma kuma lamarin ya gaggara. Bob Rugurika shugaban wani gidan rediyo wanda ya arce daga kasar bayan da gwamnatin ta nemi kamashi a wani lokacin ya yi furcin cewar.

"Da wa za a yi tattaunawar ta sulhu, domin kuwa dukkanin 'yan adawar kasar suna hijira a waje, haka su ma manya-manyan shugabannin kungiyoyin farar hula suna yin gudun hijira."

Barazanar kisan kiyashi a Burundi?

A makon da ya gabata ne dai Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da wani daftarin kudiri wanda zai bada damar aikewa da wata tawaga ta 'yan sanda na kasa da kasa domin tabbatar da tsaro a Burundi.

Burundi Ban Ki-moon & Präsident Pierre Nkurunziza

Ban Ki-moon da Shugaba Pierre Nkurunziza a Bujumbura

Ko da shike ba a bada wani karin haske ba a kan tawagar amma wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Burundi ya sanar da cewar adadin 'yan sandar zai kai zuwa 20 ko guda 30. Alhali kuwa yawancin 'yan kasar ta Burundi na bukatar ganin an tura runduna guda ta 'yan sanda a maimakon 'yan kwarorin jami'an tsaron. Claudia Simons jami'a ce ta wata cibiya ta "Kimiyya da Siyasa" ta kasar Jamus wato Gidauniyar Heinrich-Böll da kan yi aikin tabbatar da tsaro a reshen gabashin Afirka, ta ce al'ummar kasar ba su amince game da yadda 'yan siyasar ke amfani da su ba.

"Mafi yawancin al'ummar kasar ba sa son ana rarraba su ta hanyar kabilanci don yi amfani da su, amma ba wai hakan na nufin babu maganar kabilanci a kasar ba ne. Saboda shekaru 10 da suka wuce yakin basasar da aka yi fama da shi ya samo asali daga rikicin kabilanci."

Yiwuwar tashin hankali duk da lafawar rikici

Burundi Polizeigewalt - Polizei schlägt Jungen

Jami'an tsaro na ci gaba da gallaza wa jama'a

Ko da shike ya zuwa yanzu an dan samu wata 'yar kwanciyar hankali, amma dai a cikin kwanaki na gaba idan har ba a samu hanyoyin tattaunawa ba domin yin sulhu a' amura na iya kara dagulewa. Kassimi Bamba shi ne mai bai wa wakilin Kungiyar Tarrayar Afirka a Burundi da kuma yankin Grate Lakes shawara.

"A yanzu a kasar Burundi kura ta dan lafa ga halin da ake ciki, ko dai ma na ce an samu kwanciyar hankali. Amma fa ana ci gaba da yin kisan jama'a a unguwanin da 'yan adawa suke, har kullum akan sace jama'a wataran akan taras da su a ofishin hukumar leken asiri na kasar, idan kuwa ba a yi sa'a ba sai dai a tsintsi gawarsu."

Sauti da bidiyo akan labarin