Fargaban ƙasashen duniya a kan Libiya
January 27, 2016Talla
Hakan kuwa na zuwa ne kwanaki biyu bayan da majalisar Tobruk ta yi watsi da shirin gwamnatin haɗin kan ƙasa a Libiyar wanda aka cimma a makon jiya.Koblers wanda ke yin magana da 'yan jaridu a birnin Tunis ya ce ƙungiyar IS na ƙara danawa a yankin kudancin Sahara.
Abin da ke zaman barazana ta ƙara bazuwar aiyyukan ta'addanci a ƙasashen Chadi da Nijar sannan kuma ya ce a gobe za su gudanar da taron kan batun tare da Ƙungiyar Tarrayar Afirka a Habasha.