Fargaba kan rashin tsaro a Najeriya | Labarai | DW | 28.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargaba kan rashin tsaro a Najeriya

Najeriya ta ce jirgin ruwan da aka kama ɗauke da makamai, daga ƙasar Indiya ya fito

default

Hukumar kwasta a Najeriya ta ce jirgin ruwan da aka kama ɗauke da makamai ba bisa ƙa'ida ba wanda da farko ya isa ƙasar a cikin watan Yuli, ya taso ne daga ƙasar Indiya. A wannan makon hukumomin leƙen asirin Najeriya suka tsare kwantena 13 wasunsu ɗauke da rokoki da gurnati da bama-bamai da albarusai a tashar jirgin ruwa ta birnin Legas. Kame makaman ya ta da damuwa game da harkokin tsaro a ƙasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka, dake shirye shiryen gudanar da zaɓukan gama gari a farkon shekara mai zuwa, wadda kuma ta fuskanci harin bama-bamai a Abuja a ranar ɗaya ga wannan wata na Oktoba lokacin bikin cikarta shekaru 50 da samun 'yancin kai daga Turawan Ingila. A takardun jirgin dai an nuna cewa yana ɗauke da kayan aikin gine-gine ne sannan tashar ƙarshe da ya dangana kafin ya doshi Legas ita ce tashar jiragen ruwa ta Jawaharlal Nehru dake kudancin birnin Mumbai na ƙasar Indiya. Ba sabon abu ba ne jirgin ruwa ya ɗauki watanni masu yawa kafin jami'an kwasta su gama binciken kayansa a tashar jirgin ruwan ta Legas, ɗaya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa a Afirka ta Yamma.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Halima Balaraba Abbas