1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamen masoya murde gwamnati a Burkina

Muhammadou Auwal Balarabe/YBOctober 5, 2015

Wannan kuwa ya zo ne kwanaki kalilan bayan da shi jagoran juyin mulkin Janar Gilbert Diendere ya shiga hannu domin fuskantar shari'a bisa zargin laifin cin amanar kasa.

https://p.dw.com/p/1GioG
Burkina Faso Michel Kafando Staatspräsident hält Rede in Ouagadougou
Shugaba Michel Kafando mai rikon Burkina FasoHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso ta mika wa kotun sojin wannan kasa wuka da nama na binciken da za a gudanar kan juyin mulkin Gilbert Diendere da ya ci tura. Sannan kuma a karshen mako ta yi nasarar garkame biyu daga cikin manyan sojoji da ake zargi da hannu a wannan batu ciki kuwa har da Kanal Abdoulkarim Traore tsohon mai bai wa tsohon ministan harkokin waje shawara a kan al'amura na musamman.

Shi dai Janar Diendere ya yi ta nanatawa cewar zai amsa duk laifukan da ake zarginsa da aikatawa ciki kuwa har da amincewa da salwantar da rayukan 'yan Burkina faso fiye da 10 a lokacin zanga-zangar adawa da juyin mulki. Hukuncin kisa ne dai za a iya yanke wa Diendere da mukarrabansa idan aka tabbatar da wadannan laifuffuka. Sai dai kuma Hamado Dipama wani mai fafatukar tabbatar da adalaci a kasashen Afirka, ya ce kotu za ta iya yi musu sassauci.

Burkina Faso Ouagadougou General Gilbert Diendere
Janar Gilbert DiendereHoto: picture alliance/Photoshot

"Ba na jin cewar za a yanke masa hukuncin kisa, saboda daya daga cikin sharudan da ya gindaya a lokacin da ya fake a ofishin jakadancin Vatican shi ne kare ransa da na iyalinsa kafin ya fito ya mika kansa. Kasancewa kuma gwamnatin rikon kwarya na kokarin cika alkawuran da ta dauka, ina ganin cewar za a yi sassauci a hukunci da za a yanke musu, duk da cewar kundin tsarin mulki ya tanadi hukunci kisa, 'yan Burkina faso sun yi tashi tsaye don kwato hakkinsu, amma kuma sun yi iya yafe laifukan da aka yi musu."

Sai dai kuma baya ga juyin mulki da kin mika makamai, akwai wasu laifukan da ake zargin Janar Diendere da aikatawa. Na farko kuma mafi muhimmanci shi ne yawan sanya sunansa da ake yi a jerin wadanda suka taimaka wajen hambarar da gwamnatin Thomas Sankara tare da kasheshi. Sannan kuma a na zarginsa da zama kanwa uwar gami wajen haddasa fitittuna a wasu kasashe na Afirka ciki kuwa har da rikicin tawayen mali, saboda haka ne misnitan kwadagon Burkina Faso Augustin Loada ya ce makomar wannan shari'a za ta danganta da irin hadin kan da Diendere da mukarrabansa za su bayar.

Burkina Faso Spannungen Präsidentengarde
Sojoji masu tsaron fadar shugaban kasaHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

"Wannan kuwa zai danganta ne da irin halayarsa. Ya saba yin baki biy-biyu idan ya na magana. Muna fatan cewar zai fada wa kotun gaskiya a wannan karon. Muna fatan cewa zai yi wa 'yan Burkina da kuma kasashen waje karin bayani a kan duk lamuran da ake zarginsa da aikatawa."

Janar Gilbert Diendere dai na hannau daman shugaba Blaise Compaore wanda guguwar neman sauyi ta yi awon gaba da mulkinsa. Saboda ma mayar 'yan koran tsohun shugaban saniyar ware da aka yi ne, ya sa Diendere juyin mulki da ya kasa samu karbuwa. Bayan da ya lashe amansa ta hanyar sake mika wa gwamnatin rikon kwarya ta Burkina Faso ne, ya ki mika kai ga bukatar kwance damarar yakin dakaraun da ke gadin fadar shugaban kasa, sai da aka yi ta kai ruwa rana da shi ne tukuna Diendere ya mika kai bori ya hau.