Cafke wasu da ake zargi da harin Turkiya
January 14, 2016Talla
A wannan Larabar Firaministan Turkiyan Ahmet Davutoglu ya sanar da cafke wasu mutanen hudu wanda ya kawo adadin wadanda jami'an 'yan sanda ke tsare da su zuwa mutane biyar. Ana dai zargin wani haifaffen kasar Saudiya da ke da alaka da kungiyar IS mai kimanin shekaru 27 a duniya da kai harin, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 10 Jamusawa tare da raunata wasu da dama. Tuni dai ministan harkokin cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere ya ziyarci birnin na Santanbul domin ganewa idanunsa halin da ake ciki.