Fararen hula dake mutuwa a Afganistan
August 10, 2010Talla
Wani rohoton da MDD tafitar kan yaƙin Afganistan, yace kashe fararen hula ya ƙaru da kashi 30 cikin ɗari a wotanni shida na bana. Inda rohoton yace masu tada ƙayar baya, sun fi hallaka fararen hula, idan aka kwatanta da sojojin ƙungiyar tsaro ta NATO. Itama a rohoton tsakiyar shekara da ta bayar, rundunar tsaron ta dakarun ƙawance, tace tana lissafin an hallaka fararen hula fiye da dubu ɗaya a wattani shida na bana kaɗai. A jiya ne dai wata ƙungiyar agaji ta fitar da sunayen ma'aikatanta takwas, da akayiwa kisan ƙilla a arewacin ƙasar ta Afganistan, bayan da Taliban tace itace ta hallaka mutanen, domin zargin suna yaɗa kiristanci ne.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Zainab Muhammed Abubakar