1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fararen hula 50 ne suka rasa rayukansu a harin da dakarun NATO suka kai a kudancin Afghanistan.

Jami’an hukumomin jihohin kudancin Afghanistan sun ce a ƙalla fararen hula 50 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da sojojin rundunar ƙawance ta NATO suka kai a yankin a cikin wannan makon. Wani jami’in ƙaramar hukumar Panjwayi da ke jihar Kandahar ya faɗa wa maneman labarai cewa, fararen hula kusan 80 ne dakarun NATOn suka kashe a harin da suka kai wa lardin. Ita dai ƙungiyar NATOn ta ce ta sami rahotanni masu tushe, game da wannan asarar rayukan fararen hula a fafatawar da aka yi a jihar Kandahar. Amma burinta ne fatattakar ’yan ƙungiyar Taliban da ke da mafaka a wannan yankin. Ta ce dai dakarunta sun kashe mayakan Taliban ɗin 45 a ɗauki ba daɗin.