Faransawan nan shida na ƙungiyar Arche de Zoe sun koma gida | Labarai | DW | 29.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransawan nan shida na ƙungiyar Arche de Zoe sun koma gida

Ma´aikatan agajin ´yan ƙasar Faransa su shida waɗanda aka yankewa hukuncin laifin yunƙurin satar yara 103 a Chadi, sun isa gida Faransa. A cikin wannan mako wata kotu a kasar Chadi ta yankewa mutane wadanda suka hada da maza hudu da mata biyu na ƙungiyar agaji ta Zoe´s Ark hukuncin ɗaurin shekaru 8-8 da yin aiki mai tsanani a kurkuku. Gwamnatin Faransa ta nemi gwamnatin Chadi da ta miƙa mata wadannan mutanen su shida a karƙashin dokokin wata yarjejeniyar da suka cimma a shekarar 1976 wadda ta amince ´yan ƙasar Faransa da aka yankewa hukunci a Chadi da a mayar da su gida don yin zaman jarum. Ma´aikatan agajin sun ce taimako suka yi na ceto yara waɗanda aka ce wai marayu ne to amma daga baya an gano cewa iyayen su na nan da rai.