1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa zata koma kungiyar NATO

Ahmed Tijjani LawalMarch 17, 2009

Majalisar dokokin Faransa zata kada kuriá game da manufar gwamnatin na sake shigar da kasar cikin kungiyar NATO.

https://p.dw.com/p/HEMj
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, yayin da ya ziyarci sojin kasarsa dake cikin kungiyar NATO a AfghanistanHoto: AP


A ranar talata ne gwamnatin Faransa ta fuskanci ƙuri'ar amanna da manufofinta a majalisar dokoki. Dalilin haka kuwa shi ne shawarar da shugaba Sarkozy ya tsayar game da sake shigar da ƙasar ƙarƙashin tutar ƙungiyar tsaron ƙasashen arewacin tekun atlantika NATO.

Ga ƙasar Faransa, sake shigar ƙasar ƙarƙashin tutar ƙungiyar tsaro ta NATO wani muhimmin mataki ne na tarihi, kuma binciken ra'ayin jama'a da aka gudanar ya nuna cewar akasarin al'umar ƙasar na goyan bayan haka. Ga dai abin da wani daga cikin Faransawan da aka ji ta bakinsu yake cewa:


"Ya ce a haƙiƙa Faransa wani ɓangare ne na ƙungiyar NATO. Kuma a yanzun zata samu wata dama ta faɗa a ji a al'amuran ƙungiyar. Ta daɗe tana da wakilci tana kuma shiga ana damawa da ita a matakan ƙungiyar a saboda haka a ganina ba wani abin da zai canza."


Shi kansa shugaba Nikolas Sarkozy yayi imanin cewar wannan alkibla da ya fuskanta daidai ce, saboda ƙaunar da yake na ganin cewar ƙasarsa tayi tasiri a manufofi na ƙasa-da-ƙasa, wanda kuma ya sa tilas ta samu tasiri a ƙungiyar tsaron ta ƙasashen arewacin tekun atlantika. Ya dai yi bayani yana mai cewar:


"Muna tura sojoji tare da sadaukar da rayukansu, amma ba mu da ta cewa a zartarwar ƙungiyar. A yanzu lokaci yayi da zamu canza salon kamun ludayinmu. Wajibi ne Faransa ta samu ta cewa a maimakon ta riƙa karɓar umarni."


Bisa ga ra'ayin shugaban na Faransa hakan zai taimaka a ɗaga matsayin ƙasashen Turai a ƙungiyar ta NATO. Sai dai kuma tsofon P/M Dominique de Villepin mai adawa da Sarkozy ya bayyana tababa game da haka, inda ya ce wannan ba lokaci ne da ya dace ƙasar Faransa ta sake komawa tutar ƙungiyar NATO ba. Domin ita kanta duniyar, al'amuranta sun canza.


De Vellepin ya ce:"A yanzun ba ƙasashen yammaci ne ke taka muhimmiyar rawa ba, a saboda haka ba wani dalilin da zai sanya Faransa ta mayar da hankalinta akan manufofin ƙasashen yammaci a halin da ake ciki yanzun. Ba shakka a bisa taswira muna tare ne da ƙasashen yammaci da ƙungiyar tsaron tekun atlantika, amma fa ba a nan ne matsayinmu ya tuƙe ba. Muna taka muhimmiyar rawa wajen sadarwa tsakanin ƙasashen gabaci da na kudancin duniya."


Wasu daga cikin 'yan majalisar Faransa dake da ra'ayin riƙau na tattare da irin wannan ra'ayi, amma da ƙyar ne zasu ƙi yin nas'am a ƙuri'ar da majalisar zata kaɗa. Domin kuwa akwai barazanar rushewar gwamnati akan wannan matsala, inda 'yan hamayya ke ƙorafi da kakkausan harshe cewar a yanzun Faransa ta fara zawarcin Amurka tana mai watsi da cikakken ikonta na cin gashin kai.