1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa zata janye dakarun ta na musamman daga Afghanistan

Ministar tsaron Faransa Michelle Alliot-Marie ta ce kasarta zata janye daruruwan dakaru na musamman da ta girke a Afghanistan. Madamne Alliot-Marie ta ba da wannan sanarwa ne a gaban manema labarai yayin ziyarar da ta kai wa Kabul babban birnin Afghanistan. Faransa dai ta girke dakarun ta na musamman guda 200 a gabashin Afghanistan a karkashin shirin yaki da sojojin Taliban. A jimilce dai Faransa na da sojoji kimanin dubu 2 a Afghanistan wadanda ke aiki karkashin kungiyar tsaro ta NATO. Shawarar janye dakarun na Faransa dai ta zo ne a daidai lokacin da kwamnadojin rundunar ISAF a Afghanistan ke kira da a kara yawan dakaru a kudancin kasar inda mayakan Taliban suka fi karfi.