1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa zata jagoranci sojojin kiyaye zaman lafiya na mdd a Lebanon

Zainab A MohammedAugust 25, 2006

Sakatare General na MDD Kofi Annan ya bayyana cewa KTT tayi alkawarin bada gudummowan sojoji 6,900,domin fadada ayyukan kiyaye zaman lafiya na majalisar a kudancin Lebanon.

https://p.dw.com/p/BtyV
Hoto: AP
Mr Annan wanda ya sanar da hakan bayan ganawarsa da ministocin harkokin wajen kasashen turan a Brussels,yace yanzu zaa fara tattara dakarun domin turawa yankin gabas ta tsakiya.Jagoran mdd yace ya umurci faransa data jagoranci rundunar sojojin har zuwa watan febrairun shekara mai zuwa.Ya kuma sanar dacewa ya samu kasashen Malasia da Indonesia da Bangladash ,sunyi alkawarin bada gudummowan nasu sojojin zuwa kasar Lebanon.Kofi Annan yace kudurin na komitin sulhu,bai bukaci tura sojoji zuwa kann iyakar Lebanon da Izraela ba,sai dai idan gwamnatin Beirut ta nemi hakan.Ya kara dacewa,dakarun mdd bazasuje kudancin Lebanon domin kwance damarar yakin yan Hizbollah bane.