1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta fa'ɗaɗa hulɗa da Afirka

Faransa za ta inganta cinikayya da bayar da horon soji ga ƙasashen Afirka

default

Shugaba Nikolas Sarkozy na ƙasar Faransa ya amince da wasu jerin tsare - tsare, domin ƙara kyautata dangantakar ta da ƙasashen Afirka. Shugaban na Faransa, wanda ya faɗi hakan a wajen taron ƙawance tsakanin Afirka da Faransar da ya gudana a birnin Nice a kudancin Faransa ya bayyana cewar, sassan za su haɗa da na cinikayya, bayar da horo ga sojojin ƙasashen Afirka, da kuma shawo kan matsalar ɗuma'mar yanayi.

Hakanan a lokacin taron na yini biyu, shugaban na Faransa, ya bayyana buƙatar baiwa nahiyar Afirka wakilci a kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya kwatanta rashin baiwa nahiyar kujerar din - din - din a matsayin rashin adalci ne kuma abin da bai dace ba, domin a cewar sa yankin da ananne kashi ɗaya cikin huɗu na al'ummar duniya ke zaune, bai dace a ce bashi da wakilci ba a kwamitin sulhun. Kazalika ƙasar ta Faransa na ƙaunar fa'ɗaɗa harkokin ta a ɗaukacin nahiyar, maimakon mayar da hankali akan ƙasashen dake magana da harshen Faransanci kaɗai.

Shi kuwa shugaba Jacob Zuma na ƙasar Afirka ta kudu, wanda ke yin tsokaci game da taron, ya bayyana burin da nahiyar Afirka ke son cimma wajen gudanar da makamacin wannan taron kyautata dangantaka ce ya yi, inda ya ce,

" Ina ganin, abin da muke son yi - a ra'ayinmu na 'yan Afirka, shi ne daidaita sahun mu, ta yadda hakan zai dace da duk wata hulɗar da zamu yi da kowace ƙasa a duniya, ko dai da ƙungiyar tarayyar Turai ce, ko kuma da kowace ƙasa ma dake da wakilci a cikin ƙungiyar tarayyar Turai ɗin."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Ahmad Tijani Lawal