Faransa za ta bayyana takardar aihuwar Ali Bango | Labarai | DW | 12.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta bayyana takardar aihuwar Ali Bango

Hukumomin shari'ar kasar Faransa sun ba da umarnin bai wa wata daga cikin 'ya'yan marigayi Omar Bango cikakkun takardun haihuwar Shugaba Ali Bango wanda asalinsa ke haifar da mahawara a kasar ta Gabon

Hukumomin shari'a a kasar Faransa sun bada izinin bai wa wata daga cikin 'ya'yan tsohon Shugaban kasar Gabon Omar Bango Ondimba cikakkun takardun haihuwar Shugaban kasar ta Gabon na yanzu Ali Bango Ondimba.

Wannan ya zo ne a dai dai lokacin da batun asalin Ali Bango ke ci gaba da haddasa zazzafar mahawara a kasar inda masu adawa da shi ke zarginsa da yin karya a kan asalinsa .

Wannan mahawara kan asali Ali bango ta samo tushe ne daga wani littafi da wani dan jarida na kasar Faransa Pierre Pean ya wallafa inda ya ce asalin Ali Bango dan kabilar Ibo ta Najeriya ne da tsohon shugaban Omar Bango ya dauko riko a karshen yaki Biafra, batun da idan ya tabbata ka iya hana wa Ali Bangon damar sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekara ta 2016.

Shugaba Ali Bango ya musanta wannan zargi tare ma da kalubalantar dan jaridar a gaban kuliya.Yanzu dai al'ummar kasar ta Gabon ta zura ido ta ga sakamakon da takardun za su bayar