1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Za a ci gaba da yarjejeniyar Iran

Ramatu Garba Baba
May 9, 2018

'Yan majalisa a Iran sun yi bore tare da kona wata tutar kasar Amirka da aka yi da takarda a yayin zamansu na yau, suna kalubalantar matakin shugaba Donald Trump na soke yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar kasar.

https://p.dw.com/p/2xPB5
Iran Parlament Protest gegen US-Austieg aus dem Atomabkommen
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Kakakin majalisar Ali Larijani ya ce matakin babban barazana ce ga tsaro da ma zaman lafiya ya kuma baiyana shakku kan alkawarin da sauran kasashen da aka kulla yarjejeniya da su suka dauka na mutuntata.

Tuni kasashen duniya suka fara mayar da martani kan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar, inda ministan harkokin wajen Faransa, Jean Yves Le Drian ya ce, ficewar Amirka bai sa yarjejeniyar ta mutu ba, ya kara da cewa kasashen Turai na shirin ci gaba da wannan yarjejeniyar  inda ya ce za'ayi taron gaggawa a tsakanin ministocin harkokin wajen Jamus, da Birtaniya da Faransa da kuma takwaransu Iran a wannan Litinin mai zuwa. A yammancin jiya Talata ne shugaba Trump  ya sanar da soke yarjejeniyar da kuma yin alkwarin kakkaba ma Iran sabbin takunkumi.