Faransa: ′Yan sanda dubu 70 za su tabbatar da tsaro lokacin gasar Turai | Labarai | DW | 25.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa: 'Yan sanda dubu 70 za su tabbatar da tsaro lokacin gasar Turai

Dubbannen 'yan sanda za su tabbatar da tsaro a lokacin gasar cin kofin kwallon kafar Turai da za a yi a Faransa cikin watan Yuni.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve ya ce za a girke jami'an 'yan sanda fiye da dubu 70 a fadin kasar a lokacin gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Turai da Faransar za ta karbi bakwancinsa. A cikin wata hira da jaridar wasannin motsa jiki ta L'Equipe ta yi da shi, ministan ya ce za su yi duk abinda ya wajaba don hana kai wani harin ta'addanci lokacin gasar. Ya ce burin da aka sa gaba shi ne gasar ta zama wani gagarumin biki. A ranar 10 ga watan Yuni mai zuwa za a yi bikin bude gasar cin kofin kwallon kafar Turai a filin wasa na Stade de France da ke a birnin Paris, inda za a yi karawar farko tsakanin Faransa da kasar Romaniya.