Faransa tace tana cikin hadarin yiwuwar kai mata hari | Labarai | DW | 14.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa tace tana cikin hadarin yiwuwar kai mata hari

Firaministan kasar Faransa Domonique de Villepin a yau ya tabbatar da cewa,kasarsa tana cikin wani hali na hadari,bayan mutum na 2 a jerin shugabancin kungiyar Alqaed aya sanarda cewa zasu kai hari a kasar.

Ya fadawa manema labarai cewa dole ne kasar ta Faransa ta kasance cikin shiri,biyowa bayan jawabin da Ayman al Zawahiri yayi cikin sakon bindiyo da ya aike.

Cikin sakon dai al Zawahiri ya sanarda cewa kungiyar yan salaf ta GSPC dake kasar Algeria ta hade da kungiyar ta Alqaeda,yana mai kira ga kungiyar da ta zafafa adawa da takeyi da Faransa da Amurka da kuma kawayensu.

A shekarar bara kuma kungiyar ta sanarda cewa kasar Faransa itace abokiyar gabanta ta daya.