Faransa tace ba zata mika kai bori ya hau ba | Labarai | DW | 03.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa tace ba zata mika kai bori ya hau ba

Faraministan kasar Faransa, wato Dominique de villepin yace gwamnatin su ba zata mika kai bori ya hau ba ga masu bore a wajen birnin Paris. Wannan bayani dai yazo ne a bisa matsin lamba da gwamnatin ta Faransa ke fuskanta na yadda takewa wannan zanga zanga rikon sakainar kashi.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa masu zanga zangar ya zuwa yau din nan sun shafe a kalla kwanaki bakwai suna gudanar da ita.

Bugu da kari rahotanni sun nunar da cewa koda a daren jiya wayewar garin yau alhamis, sai da jamian tsaro suka yi awon gaba da wasu da yawa daga cikin masu zanga zangar.

Da yawa dai daga cikin masu zanga zangar matasa ne mabiya addinin islama.Matasan dai na gudanar da wannan zanga zangar ne don nuna bacin ransu ga gwamnatin kasar bisa wariyar launin fata da suka ce ana nunawa musulmai a kasar.