1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta yi kira ga shirya wani taron Ƙungiyar Haɗin Kan Turai don tattauna batun rikicin Lebanon.

August 20, 2006
https://p.dw.com/p/BumE

Faransa, ta bukaci ƙasar Finland, wadda ke jagorancin Ƙungiyar Haɗin Kan Turai a halin yanzu, da ta shirya wani taron ƙasashen ƙungiyar don su tattauna batun rikicin Lebanon. A cikin wata fira da ya yi da gidan rediyon France Info, ministan harkokin wajen Faransan, Phillipe Douste-Blazy, ya ce ƙasarsa na bukatar sauran ƙasashen ƙungiyar su nuna zumuncinsu ne a kan wannan batun na Lebanon. Shawarwarin da za a yi, za su dubi yadda za a tinkari batun ne a huskar siyasa, da ta soji da kuma fannin rayuwa.

Bukatar Faransan ta zo ne kwana ɗaya, bayan da shugaban ƙasar, Jacques Chirac, ya tatttauna da shugabannin ƙasashe da dama na ƙungiyar, a cikinsu har da Firamiya Romano Prodi na Italiya da Matti Vanhanen na Finland, don nanata muhimmancin tsara manufofi dallla-dala da dakarun kare zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya da za a girke a Lebanon ɗin za su yiki da su. Wata jami’ar ma’aikatar harkokin wajen Finland ɗin, ta ce Faransa ta bukaci a gudanad da taron ne a ran laraba mai zuwa a birnin Brussels. Ana dai sa ran jami’an diplomasiyya da manyan hafsoshin soji daga ƙasashe 25 mambobin ƙungiyar ne za su halarci taron.