1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta ya kamata a zabi shugaba á Lebanon ranar litinin

Bayan wani taron Ƙungiyar Tarai Taraiyar a birnin Brussels shugaban ƙasar Faransa Nicolas sarkozy yace dole ne ƙasar Lebnon ta zabi sabon shugabaan ƙasa ranar litinin. Ya kuma gargaɗi sauran kasashe da kasa su sa baki cikin harkokin zaɓen. Wannan ya zo ne a ranar da ƙasar take zaman alhinin mutuwar wani babban janar na sojanta Brigadier Francois Hajja,wanda aka kashe cikin wani harin bam a ranar laraba.Hajj shi ya jagoranci babban dauki da aka kai kan sojojin sa kai a sansanin yan gudun hijira na Palasdinawa a arewacin Lebanon a farkon wannan shekara. Akwai kuma raɗe raɗen cewa zai maye gurbin babban hafsan sojojin kasar Janar Michel Suleiman wanda shine ke kan gaba cikin yan takarar neman kujerar shugaban kasa.