Faransa ta sanarda ranakun zabe a kasar | Labarai | DW | 24.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta sanarda ranakun zabe a kasar

Gwamnatin kasar Faransa ta sanarda ranakun da zaa gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa.

Tace ranar 22 ga Afrilu zaa yi zabe na farko,zagaye na biyu kuma makonni biyu baya,wato ranar 6 ga watan mayu.

Zaa kuma gudanar da zabukan majalisar dokoki ta kasar a ranakun 10 da kuma 17.

Karkashin gyara da akayiwa kundin tsarin mulkin kasar 2000, wadda kuma ya rage waadin shugaban kasa zuwa shekaru 5 daga shekaru 7,an amince cewa,yan majalisa da shugaban kasa wadin su zau kare tare.

Manyan abokan hamaiya a zaben sun hada da ministan harkokin cikin gida Nicolas Sarkosy na jamiyar UMP mai mulki da kuma Segolone royal na jamiyar Socialist kodayake baa riga an baiyana tsayawarsu takara ba.

Shugaba Jaque Chirac wanda ke mulkin Faransa tun 1995,ya baiyana yiwuwar sake tsayawarsa takara karo na uku,kodayake kurair jin raayin jmaa da aka gudanar ya nuna cewa,da kyar ne a zabe shi.