1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta ce za ta sa ƙafar wando ɗaya da masu ta da zaune tsaye a ƙasar.

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueN

A jajiberen ranar cika shekara ɗaya da tarzoman nan da ta addabi manyan biranen Faransa da dama a bara, an sami aukuwar tashe-tashen hankulla da dama a birnin Paris da kewayensa. A cikin darten jiya kawai, rahotanni sun ce wani gungun matasa ya afka wa bas-bas guda huɗu, inda matasan suka cinna musu wuta. A karo ɗaya ma, sai da matasan suka yi wa direban wata bas da fasinjoji da suke ciki barazanar harbe su da bindigogin da ke hannunsu. Sai dai an auna arziki ba a kai ga hakan ba. Rahotanni sun ce babu ma wanda ya ji rauni. Sai dai matasan sun tilasa wa direban da fasinjojin sauka daga bas ɗin ne kafin su cinna mata wuta.

Firamiyan Faransan, Dominique de Villepin, ya bayyana matuƙar ɓacin ransa game da wannan lamarin. Ya ce gwamnatinsa ba za taɓa nuna sassauci ga waɗannan masu aikata miyaguin laifuffuka ba. Ya kuma yi kira ga ɗaukan tsauraran matakai don hukuntad da waɗanda za a samu da laifin:-

„Ba za mu taɓa amincewa da wanzuwar wani yanki a cikin ƙasarmu inda babu doka da oda. Burinmu ne mu tabbatad da cewa, a ko’ina cikin ƙasarmu, dokoki na bai ɗaya ke aiki, inda za mu bai wa kowa tabbacin kare hakkinsa.“