1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta bukaci taron shugabanni kan Ukraine

Yusuf BalaSeptember 7, 2015

Shugaba Holland ya ce makwannin baya-bayan nan alamu na nuna cewa bangarorin da ke gaba da juna suna mutunta yarjejeniyar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1GSAP
Frankreich Pressekonferenz Präsident Hollande
Shugaba HollandHoto: Reuters/P. Wojazer

Shugaba Francois Holland na Faransa ya bayyana bukatar yin wani taro tsakanin shugabanin kasashen na Faransa da Jamus da Rasha da Ukraine . Taron da a fadar shugaba Holland za a yi a birnin Paris za a yi shi ne nan gaba kadan cikin wannan wata inda za a sake nazarin ci gaban da aka samu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla wa rikicin kasar ta Ukraine.

Da yake jawabi ga taron manema labarai shugaba Holland ya ce makwannin baya-bayan nan alamu na nuna cewa bangarorin da ke gaba da juna suna mutunta yarjejeniyar.

Ya ce ministocin harkokin wajen kasashen zasu tattauna kwanaki da ke tafe sannan kuma shugabannin kasashen su tattauna a ranar 28 ga watan nan na Satimba dan duba hanyoyi da zasu kai ga karshen rikicin da ke tsakanin kasashen.