Faransa ta buƙaci Isra′ila ta girmama sakamakon binciken harin Gaza | Labarai | DW | 06.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta buƙaci Isra'ila ta girmama sakamakon binciken harin Gaza

Sai dai Isra'ila tace ba zata amince da duk wani bincike na ƙasa da ƙasa ba.

default

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy yayi kira ga Firaministan Isra'ila daya girmama sakamakon rahoton binciken harin da sojojin Israila suka kai akan wani jirgin 'yan agajin taimako dake kan hanyar sa ta zuwa Gaza.

A tattaunawar da yayi da Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu ta wayar tarho, Sarkozy yace Faransa a shirye take ta shiga cikin binciken.

Shugaban na Faransa ya kuma jaddada buƙatar sake komawa zauren sulhu tsakanin Isra'ilan da Palasɗinawa da nufin samun kafuwar ƙasashe biyu masu 'yancin kai.

Sai dai duk da wannan kira na shugabanin ƙasashen duniya Isra'ila tace zata gudanar da bincike na kanta da kanta. Jakadan Isra'ila a Washington yace Isra'ila bazata amince da duk wani bincike na ƙasa da ƙasa ba.

Harin da Sojojin Isra'ila suka kai cikin wani jirgin 'yan agajin Gaza yayi sanadiyar mutuwar mutane 9 ciki harda ba'amirka guda.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita:Umaru Aliyu

AFP