Faransa ta ba da umarnin ƙasa da ƙasa na kame wasu jami’an gwamnatin Rwanda. | Labarai | DW | 21.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta ba da umarnin ƙasa da ƙasa na kame wasu jami’an gwamnatin Rwanda.

Wani jojin Faransa, mai gudanad da bincike kan kisan gillan da aka yi wa shugaban ƙasar Rwanda, Juvenal Habyarimana, ya ba da umarnin ƙasa da ƙasa na kamo wasu jami’an gwamnatin Rwandan, masu kusanta da shugaban ƙasar na yannzu Paul Kagame. Harbo jirgin saman tsohon shugaba Habyarimana da aka yi a shekarar 1994 ne ya janyo mummunan kisan kiyashin da aka yi a ƙasar a wannan shekarar. Kamfanin dillancin labaran nan Associated Press, ya ruwaito daga birnin Paris cewa, jojin, Jean-Louis Brugiere, ya sami amincewar masu jami’an ɗaukaka ƙarar ƙasar wajen ba da umarnin. A cikin waɗanda Faranmsa ke nema dai har da wasu manyn janar-janar guda biyu na rundunar sojin Rwandan. Tun shekarar 1998 ne dai iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harbo jirgin samman da aka yi, suka ɗaukaka ƙara gaban kotu a Faransa.