Faransa ta aika sojoji a Nijar | Labarai | DW | 20.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta aika sojoji a Nijar

Gwamnatin Nijar ta ba sojojin Faransa izinin amfani da sararin samaniyar ƙasar wajen ƙwato mutanen da Aqmi ke garkuwa da su

default

Sojojin Faransa

Hukumomin ƙasar Nijar sun bada izini ga sojojin Faransa da su yi amfani da sararin samaniya ƙasar domin ƙwato wasu ma´aikata kamfanin Areva guda bakwai wanda biyar daga cikin su faransawa ne da wasu mutanen da ake kyautatan zaton cewa ´yan ƙungiyar Alƙ´aida ne reshen Aqmi suka sace su kuma su ke yin garkuwa da su a cikin hamadar da ke a yankin arwacin ƙasar. Wannan izini wanda shine karo na farko a cikin shekaru 25 da gwamnatin ƙasar Nijar ta bayar ga Faransa ya sa yanzu haka sojoji kamar guda 100 na ƙasar ta Faransa waɗanda su ka ƙware ta fannin yaƙi da ta'adanci sun isa a birnin Yamai a cikin jirage na yaƙi da dama. Mawallafi: Abdourahman Hassane

Edita: Yahouza Sadissou Madobi