1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Suka

YAHAYA AHMEDNovember 16, 2005

Jawabin da sshugaban kasar Faransa, Jacques Chirac ya yi wa al'umman kasarsa a kan talabijin, bai sami karbuwa a bainar duk jama'a ba. `Yan siyasa da dalibai na cikin wadanda suke yi masa suka.

https://p.dw.com/p/BvUP
Shugaban Faransa
Shugaban FaransaHoto: AP

Jawabin da shugaba Jacques Chirac na Faransa ya yi ga al’umman kasarsa a kan talabijin, shi ne batun da masharhanta suka fi mai da hankalinsu a kai a birnin Paris. Shugaban dai, ya yi kira ne ga girmama juna, amma kuma ya nanata muhimmancin da kiyaye dokokin kasar ke da shi, da kuma shirin gwamnatinsa na yakan salon nan na bambancin launin fata. Matasan Faransan, mafi yawansu `ya`yan baki ne rikicin kwanakin bayan nan ya fi shafa. Kamar dai Leila, wata dalibiya balarabiya da ke zaune da kuma karatu a birnin Lyon, wadda ta ce ta saurari duk jawabin shugaban kasar, sa’annan ta bayyana ra’ayinta kamar haka:-

„Shugaban dai ya zayyana irin bacin ran mazauna unguwannin wajen manyan buiranen dalla-dalla. Daga jawabinsa dai, kowa zai iya gane cewa Faransan ta kasu ne a gida biyu, a halin yanzu. Wato akwai Faransa ta tsantsa, da kuma Faransa ta unguwannin wajen manyan birane, inda mazauna cikinsu, ba su da inda za su mai da alkiblarsu. Kamata ya yi, su ma, a samar musu hanyoyin da za su iya hangen makoma ingantacciya.“

Ba a bainar dalibai kawai ne ake suka ga jawabin da shugaba Chirac ya yi ba. A da’irar `yan siyasa ma, an yi kakkausar suka ga shugaban, wanda bai ce uffan ga tashe-tashen hankullan ba, sai fiye da bayan makwanni biyu tukuna. Wani dan majalisa na bangaren `yan adawan kasar ya bayyana cewa:-

„Na kosa da irin wannan gibin da ake samu tsakanin kyawawan kalamu da aikata wani abu a zahiri. A cikin jawabin Chirac, za mu iya tunawa ne da batun tabarbarewar halin rayuwar jama’ar kasar nan, wanda ya yi jawabi a kai shekaru 10 da suka wuce. Amma tun wannan lokacin, babu wani matakin da ya dauka, a mukaminsa na shugaban kasa, don rage gibin da ke ta kara fadi tsakanin nau’i daban-daban na al’ummar kasar nan.“

Duk da sukar da `yan adawar ke yi wa gwamnatin shugaba Chirac dai, da kuma ka da kuri’un da mafi yawansu suka yi a majalisa, na kin amincewa da tsawaita lokacin dokar ta bacin har zuwa watanni 3 nan gaba, hakan bai hana kudurin samun karbuwa ba. `Yan majalisa dari 3 da 50 ne suka amince da shirin, sa’annan dari da 50 kuma suka wancakalar da shi. Wata `yan jam’iyyar Greens a majalisar, Noel Mamere, wadda jamdiyyarta ma ke adawa da shirin, ta bayyana cewa:-

„Matsayin da muka dauka dai ta nuna adawa ne a bai daya, ga shirin tsawaita lokacin dokar ta bacin. Wato shirin, kamar dora murfi ne kann tukunya, wadda ruwa ke tafasa a cikinta. Ba ta danniya, da anagaza wa jama’a bin doka da oda da tsoratad da mutane ne za a iya shawo kan matsalolin unguwannin wajen biranen ba. Ta tuntubar juna ne kawai za a iya warware matsalar.“

Kurar rikicin dai na lafawa sannu a hankali. Amma duk da haka, a ko wane dare, sai an sami motoci da bas-bas da aka cinna wa wuta. A daren jiya kawai, rahotanni sun ce kusan motoci dari da 60 ne aka kokkona. Jami’an tsaro kuma sun kame mutane 44. Haka ne dai alkaluman da `yan sanda suka bayar ke nunawa.

A lokacin da ba a sami hauhawar tsamari kamar na yanzu ba ma, kusan motoci dubu 2 da dari 8 ne ake cinna wa wuta a ko wane wata. Tun daga farkon wannan shekarar kawo yanzu, yawan motocin da aka kokkona a tashe-tashen hankulla a Faransan ya kai dubu 28. Amma ba a kai ga kololuwar tarzomar ba, sai makwanni biyu da suka wuce, inda matasa, a galibi `ya`yan baki makaurata, suka dinga bayyana damuwarsu a zahiri. Boren matasan dai na da nasaba ne da rashin gamsuwarsu game da yadda ababa ke wakana, da rashin kaunar da suke ganin ana nuna musu, da kuma hangen da suke yi na cewa babu ma mai bukatarsu a kasar.

Kamfanonin inshwara dai sun ce, barnar da ta auku sakamakon wannan rikicin, ta kai kimanin Euro miliyan dari biyu da 40 a kudance. Tuni dai shugaba Chirac ya tabbatar cewa:-

„Za a gaggauta shirin biya wa wadanda suka yi asarar kadarorinsu diyya. Kazalika kuma, ina yi musu jaje da tabbatar musu zumuncin duk kasa baki daya.“