Faransa: Rayuwa mai tsauri a sansanin bakin haure
Kusa da Dunkirk ana tsallaka ruwa sai Birtaniya, bakin haure suna zaman jira na rashin tabbas a dakunan kara a sansani a Faransa. Yayin da jami'ai suka ba da baya kimanin Kurdawa 2000 suka fata bisa kai wa ga Birtaniya.
Wanka da laka
Rayuwa a cikin kananan tantuna, kimanin mutane 2000 da suka hada da maza, da mata, da kuma yara ke rauywa a sansani Grande Synthe ba a hukumance ba kusa da Dunkirk. Ruwan sama ya mayar da wurin laka ga sanyi da daddare.
Hakuri
Lizman, daga yankin Kurdawa mai kwarya-kwaryar 'yanci na arewacin Iraki, yana son isa Birtaniya. Ya ce akwai yaki a inda ya fito. A cikin karamin daki yana hada "cafe" inda matasa suke haduwa yayin da suke zaman jira.
Kai wa ga Birtaniya
Asis ya yi aron guduma domin gyara tanti saboda kare sanyi. Matashin yana tsarin kai wa Birtaniya, inda ya ce "abubuwa za su inganta." Zai biya masu safarar mutane kimanin 5000 na Eurodomin samun wucewa zuwa Ingila ta bututu.
Wata fata
Babu wanda yake da masaniya kan yawan yaran da ke sansanin. Ma'aikatan jinkai kan karbi dabbobi na wasa, kuma daga lokaci zuwa lokaci suna suna raba kayan wasa ga yara a wasu kebabbun tantuna.
Watsarwa
Yaro dole ya rasa abun wasa, yanzu yana cikin laka. Fata mai yawa na dushashewa a sansanin, inda ake samun matsananci sanyi da daddare, ga duhu ba haske. Mazauna wurin suna da bayan-gida takaitattu.
Taimako daga Ingila
Tsohon jami'in soji Chris Bailey na Birtaniya da ya taba zama a Iraki yanzu yana taimakon bakin haure da suke son isa kasarsa ta Birtaniya, ya bayar da mayafi da takalma. Tsohon sojin ya ce "Yanayin da suke ciki yana sukurkucewa fiye da abin da na gani a wajen yaki."
Barka da zuwa Faransa
Denise (a hannun hagu) da Maryse suna da kalami gami da shayi ga bakin haure. Suna rayuwa a wani gida da ke bangare daya na hanya- wannan hanya ta raba bangarorin biyu. Denise ya ce "Hukuma ba ta kula da su. Ya kara da cewa sauran makwabta suna son kawo karshen bakin hauren.
Ina 'yan siyasa?
Wani mai aikin sa-kai ya saka sunan 'yan siyasan Turai: Misali titin Francois Hollande, saboda gwamnatin Faransa ba ta kula da sansanoni wadanda ba a hukumance suke ba. 'Yan sanda ba sa shiga ko akwai rahotannin tashin hankali.
Abinci mai zafi daga Jamus
'Yan kalilan na bakin haure sun isa birnin Munich na Jamus, sai dai Sinan von Stietencron na gidan abincin VolxKüche da ke Munich yana taimakon bakin hauren da ke Faransa, wadanda ya ce suna cikin yanayi na bukata.
Ingantawa
Masu ba da agaji daga kungiyar likitoci na gari na kowa suna rigakafin wasu cutuka. Sabado yanayin wurin ana samun mura, hakan na sa yara su galabaita. Gwamnatin ba ta yi musu komai, suna gina wajen kula da lafiya na gaggawa da ke zama na farko a Turai.
Wajen zama a lahira
Asim, wanda ya tsere wa Daular Islama a Iraki, ya samu labewa. Ya tsara inda ya ke zama kuma ya tsaftace shi. Mutumin ya gayyaci Catherine Martens wakiliyar DW inda ya ba ta shayi. Ya ce "Kowa ya matsu da ya wuce."
Mai zai faru a gaba?
Gaban ruwan Dunkirk yana da nisan kilo-mita 10 daga sansanin, amma damar isa Birtaniya babu yawa. Kadan ne suke neman mafaka a Faransa. Zabin da suke da shi na zaman amfani da masu fasakwauri ko kuma zuwa Belgiyam ko Jamus ko zaman jira.