1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Kasashen Turai su guji mulkin mulaka'u

Yusuf Bala Nayaya
April 17, 2018

Faransa ta bukaci kasashen Turai su kare demokradiyya don kauce wa kama karya da rashin martaba demokradiya mai 'yanci da ake gani a wasu manyan kasashen duniya ciki har da masu da'awar mulki na gari.

https://p.dw.com/p/2wD3n
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron yana jawabiHoto: Reuters/V. Kessler

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi kiran takwarorinsa na Turai su kare martabar demokradiyya mai 'yanci, yayin da ake kara samun masu kama karya a fadin duniya da wadanda ba sa martaba demokradiya mai 'yanci ko da a tsakanin kasashen na Kungiyar Tarayyar Turai. A lokacin da ya ke jawabi a gaban majalisar Tarayyar Turai a Strasbourg da ke arewacin Faransa, shugaban Macron wanda ya samu yabo da tafi na wasu 'yan majalisa a lokacin da ya ke jawabin da ya kushe masu tsattssauran ra'ayi da ke samun tagomashi ko da a cikin Turai wajen kare Turai daga al'umma, da ma siyasa mara sassauci.

Frankreich Präsident Emmanuel Macron mit Militärs | Syrien-Krieg
Hoto: Reuters/F. Guillot

A kaikaice shugaba Macron na shagube ga kasashe irinsu Hangari da mahukuntanta ke nuna kin baki ‘yan kasashen waje karara, ya ce manufarsu ba ta da kyau musamman ga makomar hadakar kasashen na Turai a lokacin da suke tunkarar matsaloli irinsu sauyin yanayi da kwararar baki da kokari na mamayar manyan kamfanoni da gwamnatocin 'yan babakere, inda ya kawo misali da kasashen irinsu China da Rasha  da ma babbar kawa ga kasashen na Turai wato Amirka da ke neman zama daga ita sai 'ya'yanta.

Shugaba Macron ya kuma yi kira ga takwarorin nasa na Turai da su gaggauta amincewa da tsarin da zai kawo sauyi a kudin euro, da harkokin tattalin arziki na bai daya da suke da shi. Shugaba Macron  ya ce Faransa na shirye ta kara yawan kasafin abin da take bayarwa a kungiyar Tarayyar Turai ta yadda kasafin zai inganta

Wannan kasafin kudi da za mu tattauna a kansa, sai ya tabo tsare-tsaren siyasa cikin daidaito da kargo da hadin kai. Faransa ta shirya kara yawan abin da take bayarwa zuwa kasafin na Tarayyar Turai. Amma yin hakan na nufin sake girka ginshikin kasafin da kansa da dole a duba shi.

Bulgarien Jean-Claude Juncker in Sofia
Jean-Claude Juncker Hoto: picture alliance/dpa/AA

Shi kuwa shugaban hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker da ya ke mayar da martani bayan jawabin Shugaban na Faransa a gaban majalisa, ya yaba wa shugaban kan yadda ya mayar da hankali kan kungiyar ta kasashen Turai inda ya ce Faransa ta asali ta dawo; ya ce zabin nasa ya kara sabon karfin gwiwa ga kungiyar.

Na yi maraba da dawowar Faransa a cikinmu, sannan zan iya cewa zabenka a matsayin shugaban Faransa da ma yakin neman zabenka ya ba wa kasashen Turai sabon karfin gwiwa. Ina fatan burin da ka sanya a gaba zai zamo nasara. Ka saka a zuciyarka cewa hukumar Tarayyar Turai na goyon bayanka kan abin da ka sanya a gaba.

Juncker ya yi gargadin cewa Kungiyar Tarayyar Turai na bukatar ta bude kofarta ta kara karbar sabbin mambobi daga yankin yammacin Balkans don kauce wa kasadar fadawa sabon yaki a yankin.