1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Karon batar karfe tsakanin Macron da Le pen

Gazali Abdou Tasawa
May 7, 2017

Al'ummar Faransa na ci gaba da kada kuri'ar a zaben shugaban kasa zagaye na biyu a wannan Lahadi inda ake fafatawa tsakanin Marine Le Pen 'yar shekaru 48 da kuma Emmanuel Macron dan shekaru 39.

https://p.dw.com/p/2cYTk
Frankreich präsidentschaftswahl Plakte Macron Le Pen
Hoto: Reuters/R. Pratta

Tuni dai Emmanuel Macron ya kada kuri'ar sa a garin Le Touquet a yayin da Marine Le Pen ta kasance a karamar hukumar Henin-Beaumont in ta kada kuri'a. Ofishin ministan cikin gida na kasar ya bayyana cewaR ya zuwa tsakiyar ranar ta yau adadin mutanen da suka fito zaben ya kai kaso 28,23% na wadanda suka cancanci kada kuri'ar ta su. Hasashen jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan sun bayyana Emmanuel Macron a matsayin wanda zai lashe zaben da kaso 61,5%.

 Sai dai nasarar ba zata da Donald trump ya samu a zaben Amirka da ma yadda masu goyon bayan ficewar Birtaniya daga Kungiyar EU wato Brexit suka samu ta sanya Faransawar da dama yin taka tsantsan a game da hasashen jin ra'ayin jama'a musamman a game da fargabar da ake da ta yiwuwar samun mutane da dama da za su yi rowar kuri'un su.