Faraministan wucin gadi a Pakistan ya fara aiki | Labarai | DW | 16.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faraministan wucin gadi a Pakistan ya fara aiki

Shugaba Pavez Musharraf na Pakistan ya rantsar da Mr Mohammadmian Soomro , a matsayin sabon Faraminista na wucin gadi. Rantsuwar ta Mr Soomro ta zo ne awowi kaɗan, bayan sakin Benazir Bhutto ne daga ɗaurin talala da ake mata. Ana sa ran Mr Soomro zai jagoranci yadda za a gudanar da zaɓen gama gari ne da ake shirin gudanarwa, a watan Janairun sabuwar shekara. Kafafen yada labarai dai sun rawaito Mr Musharraf na assasa bayanin dawo da Pakistan turba ta Dimokruɗiyya.

Mr. Musharraf ya ce yana da kyau muyi alfahari cewa a yanzu Pakistan ta kama turbar mulkin Dimokruɗiyya. Duk da cewa ni soji ne, ina alfahari da yadda na karkata akalar ƙasar, izuwa turba ta Dimokruɗiyya.Tuni dai tsoffin Faraministocin ƙasar biyu, wato Benazir Bhutto da Mr Nawaz Sharif suka cimma yarjejeniyar kalubalantar Mr Musharraf, a fagen zaɓen gama garin.