FARAMINISTAN ISRAELA YA KARA SHIGA CIKIN MAWUYACIN HALI. | Siyasa | DW | 04.03.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

FARAMINISTAN ISRAELA YA KARA SHIGA CIKIN MAWUYACIN HALI.

Faraministan kasar Bani Israela Arial sharon a yanzu haka naci gaba da fuskantar mawuyacin hali daga mutanen kasar sakamakon dangantaka da aka gano yake da ita dangane daya daga cikin mutanen da Kungiyyar Hezboullah tayi musayar Fursunoni dashi a watan daya gabata.

Rahotanni dai daga kasar Sun tabbatar da cewa Arial sharon nada alaqa da Surukin Elhanan Tannenbaum,wanda kungiyyar Ta herzboullah ta sako a maimakon fursunoni Palasdinawa da kasar ta Bani israela ita ma ta sako musu a matsayin ban gishiri in baka manda.

Bugu da kari Rahotannin sun nunar da cewa Shimon Cohen dan shekara 89,wanda yake suruki ne ga El hanan ya kasance daya daga cikin mutane da suka taba yiwa Arial sharon aiki a gonar sa a shekara ta 1970.

To babban abin tambaya a nan daga mutanen kasar ta bani israela shine,wane dalili ne yasa Faraministan bai shaidawa majalisar ministocin sa ko kuma mutaken kasar cewa yana da alaka da surukin daya daga cikin mutanen da aka sako ba bisa wan nan yarjejeniya a tsakanin kasar da Kungiyyar Hezboullah kann batun musayar fursunonin.

A cikin wata kuriar neman jin raayi da wata jaridar kasar mai suna Maariv ta gudanar a kasar ta nunar da cewa kashi 42 daga cikin dari na mutanen da suka kada kuriar sun nemi da faraministan ya sauka daga madafun ikon kasar bisa wan nan zargi da ake masa.

Kana a hannu daya kuma kashi 43 sunce basu goyi bayan ya sauka ba,to amma kuma sun soki lamirin shugaban da boye gaskiya dangane da dangantakar da yake da ita a tsakanin sa da surukin Elhannen Tannenbaum.

Jaridar taci gaba da cewa Cohen ya tabbatar mata da cewa Arial Sharon ya dade yana nuna yabo a gareshi to amma kuma sun dade basu sadu ko kuma ji daga juna ba.

A daya barin kuma a jiya laraba ne Faraminista Sharon ya fito gidan daya daga cikin talabijin din kasar yana fadin cewa ba zai sauka daga mukamin sa ba kann wan nan abu da ake zargin sa a kai.

Domin a cewar sa bashi da wani abu da zai boye dangane da ko yana da alaka da Cohen ko kuma akasin hakan.

A ma dai karshe Sharon cewa yayi wan nan kinibibi ne kawai ake shirya masa ba don komai ba illa kawai a bata masa suna.

A yanzu haka dai da dama daga cikin bani yahudun na cike da tunanin yadda wan nan al,amari ya faru,musanmamma kann batun musayar fursunonin a tsakanin kasar da kuma kungiyyar ta Hezboullah,kann mutane uku daya mai rai biyu kuma gawa,a mai makon sama da mutane 400.

Wan nan a yanzu haka ya haifar da dama daga cikin yan kasar na tambayar kansu shin mema ya kai Elhannen izuwa iyakar kasar ta Lebanon,wanda hakan ne yasa mambobin kungiyyar ta Hezboullah suka kama shi.

A dai tun lokacin daya dawo yake fuskantar tuhuma na dalilin hakan da kuma inda aka kaishi bayan kame shin daga bangaren jamian tsaron kasar.

Tuni dai Elhanen ya shaidawa jamian tsaron cewa mambobin na hezboullah sun cafke shine bayan ya dawo daga kai ziyara izuwa birnin Dubai a kann hanyarsa ta dawowa gida.