Fara tattauwar daukar Turkiya cikin kungiyar EU | Siyasa | DW | 16.12.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fara tattauwar daukar Turkiya cikin kungiyar EU

Akwai sabanin ra´ayi tsakanin kasashen kungiyar tarayyar Turai dangane da cancantar daukar kasar Turkiya cikin kungiyar EU.

Masu goyon bayan fara tattaunawar daukar kasar Turkiya cikin KTT na da ra´ayin cewa tuni kasar ta fara aiwatar da canje-canje na demukiradiyya, da girmama hakin dan Adam da kuma soke hukuncin kisa a cikin kasar. Amma masu sukar lamirin kasar ta Turkiya na zargin cewa kasar mai yawan al´umar musulmi ta fi kusa da yankin Asiya.

Alal misali wata kuri´ar jin ra´ayin jama´a da aka gudanar a kasar Faransa ta nunar da cewa kashi 75 cikin 100 na al´umar kasar na adawa da shigar da Turkiya cikin kungiyar EU, musamman ganin yadda ake daukar kasashe fiye da kima a cikin kungiyar. Kasar Faransa na fargabar wani tasiri da musulmi zasu yi cikin EU idan aka dauki Turkiya mai yawan al´umar miliyan 70 a wannan kungiya. Da dama a cikin ´yan siyasar kasar na ganin yanzu maganar ma daukar Turkiya cikin EU sam ma ba ta taso ba, kamar yadda dan jam´iyar dake jan ragamar mulki a Faransa Dominique Paillet ya nunar yana mai cewa a kan taswira Turkiya ba ta cikin nahiyar Turai, sannan a tarihi ma kasar ba ta da wata alaka da Turai.

Ita kuwa Elizabeth Guigou ´yar jam´iyar ´yan Socialist cewa ta yi bai kamata a rufewa Turkiya kofar shiga cikin kungiyar EU ba. Yanzu kasar ta Faransa zata gudanar da kuri´ar raba gardama akan wannan batu, kamar yadda shugaba Jacques Chirac ya nunar.

Su kuwa ´yan kasar Britaniya ba su da ra´ayi gudanar wata kuri´ar raba gardama, domin tuni FM Tony Blair ya yi maraba da shirin fara tattaunawa da Turkiya din da nufin daukarta cikin kungiyar EU. Ga ´yan Britaniya yanzu lokaci yayi da ya kamata a sakawa Turkiya wadda tun kimanin shekaru 40 da suka wuce take kokarin samun karbuwa a nahiyar Turai. Masu goyon bayan wannan mataki a Britaniya na nunar da cewa ita ma kungiyar EU zata ci riba idan ta dauki Turkiya cikin ta, yayin da hakan kuma zai taimaka a shimfida sahihiyar demukiradiya tare da girmama hakkin dan Adam a Turkiya, don zama abar koyi ga sauran kasashen musulmi. Hakazalika hakan zai taimaka nahiyar Turai ta fadada angizonta, inji Michael Ancram dan jam´iyar adawa ta Conservative.

A sabbin kasashen kungiyar ta EU kamar a tsoffafin kasashen fara tattaunawar daukar Turkiya cikin kungiyar na taka muhimmiyar rawa a harkokin siyasar wadannan kasashe. Gwamnatocin kasashen Hungary da Czeck da Slovakiya da kuma Poland ba sa nuna adawa da fara wannnan tattaunawa da kasar ta kudu maso gabashin nahiyar Turai. To amma Poland ta fi son a yi haka da makwabtanta wato kamar Ukraine da Belarus.

Su kuwa a nasu bangaren kasashen Hungary da janhuriyar Czeck da kuma Slovakiya ba sa kalubalantar shigar da Turkiya cikin kungiyar EU, duk da cewa tarihi ya nuna da akwai dan rashin jituwa tsakanin Turkiya din da wadannan kasashe, amma hakan ba zai yi wani tasiri na ku zo ku gani akan wannan manufa da aka sanya a gaba ba.

 • Kwanan wata 16.12.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveA
 • Kwanan wata 16.12.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BveA