Fara aikin yajejeniyar Lissabon | Siyasa | DW | 01.12.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fara aikin yajejeniyar Lissabon

A yau ne ƙasashen Turai zasu fara aiki da yarjejeniyarsu ta Lissabon

default

Shugabanni da ministocin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai

Yau dai kimanin shekaru takwas ke nan da shuagabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai suka gudanar da wani taron ƙoli don tsayar da shawara akan wani kundin tsarin mulkin da zai zama gishiƙin ayyukan ƙasashen ƙungiyar. Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi, a yau talata yarjejeniyar ta Lissabon zata fara aiki. To ko wani abu ne sabo game da yarjejeniyar.

Eu Flagge Flash-Galerie

Tutar Ƙungiyar Tarayyar Turai

Taken ƙasashen Turai daga kiɗan Beethoven da shuɗiyar tuta mai taurari 12, waɗanda aka yi shekara da shekaru ana amfani da su a matsayin alamar haɗin kai tsakanin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai, a ƙarƙashin yarjejeniyar ta Lissabon, ba za a ci gaba da amfani da su a hukumance ba. A sakamakon matsin lamba daga ƙasashen Birtaniya da Poland, wajibi ne a yi fatali da duk wani abin dake yin nuni da kasancewar Turai, wata ƙasa ɗaya, al'uma ɗaya. Kungiyar zata ci gaba ne da kasancewa wata gamayya ta haɗin kan ƙasashe kawai. Ƙungiyar ba zata wayi gari a matsayin wata tarayya ta ƙasashe ba, in ji Christoph Möllers daga jami'ar Humboldt dake birnin Berlin.

"Wata ƙasa ta tarayya ba ta cikin tsarin ƙungiyar tarayyar Turai. Saboda ƙungiya ce dake magana da yawun ƙasashenta akan wata sibga ta dogon turanci kuma ƙasashen na da gagarumin tasiri a manufofinta. Al'amuranta na da sarƙaƙiyar gaske ta yadda ma za a iya cewa tayi daura da tsarin mulki na demoƙraɗiyya tsantsa, kamar yadda aka saba a ɗaiɗaikun ƙasashe. Ita kanta ma dai ba za a iya kwatanta ta da sauran ƙasashe a wawware ba."

Yarjejeniyar ta Lissabon, wadda ta samu sakamakon tattaunawa ta tsawon shekaru takwas, tana ba wa wakilan majalisar Turai da aka zaɓa kai tsayi ƙarin ikon faɗin albarkacin bakinsu a dukkan batutuwa na siyasa daidai da wakilan majalisun ministocin ƙasashen ƙungiyar su 27. An saurara daga bakin Jo Leinen, wakili a majalisar Turai kuma tsofon shugaban kwamitin nazarin kundin tsarin mulkin ya bayyana farin cikinsa game da haka inda yake cewar:

Plenarsaal EU Parlament

Majalisar Turai

"Majalisar Turai na daga cikin waɗanda suka ci gajiyar wannan sabon garambawul. A yanzu zamu yi kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnatoci da majalisun ministoci, waɗanda kawo yanzu suke da babban angizo a Ƙungiyar Tarayyar Turai. Hakan na ma'ana ne cewar, Brussels ba zata iya zartar da wata doka ba tare da amincewar majalisar Turai ba."

Yarjejeniyar ta Lissabon ta naɗa sabbin shugabanni. Da farko Herman Van Rompuy, P/M Belgium, wanda aka naɗa sabon shugaban Kwamitin zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai don shekaru biyu da rabi masu zuwa. Wannan kwamitin dai shi ne ke tsayar da shawara akasn alƙiblar siyasa da ƙungiyar zata fuskanta. Sai kuma Baroness Catherin Ashton, wadda zata wakilci ƙungiyar a manufofi na ƙetare da tsaro don shekaru biyar masu zuwa. Dukkan jami'an siyasar biyu dai ba a sansu a fagen siyasar duniya ba. Wani abin da yarjejeniyar ta Lissabon wadda aka rattaɓa hannu kanta shekaru biyu da suka wuce a birnin Lissabon ta ƙunsa kuma shi ne wata dama ta ƙuri'ar raba gardama, kuma a karo na farko ƙasashe na iya ficewa daga tutar ƙungiyar ta tarayyar Turai.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abdullahi Tanko Bala