Falasdinawa akalla 4 sun rasu a wani harin makami mai linzami | Labarai | DW | 20.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasdinawa akalla 4 sun rasu a wani harin makami mai linzami

Sojojin Isra´ila sun harba wani makami mai linzami akan wata mota a birnin Gaza inda suka halaka akalla Falasdinawa 4 ciki har da wani kwamandan kungiyar Jihadin Islami, sannan suka jikata mutum biyar. Motar tana tafiya ne a kusa da gidan ministan harkokin wajen Hamas Mahmoud Zahar lokacin da aka kai mata harin. Da farko majiyoyin tsaro da na asibiti sun ce makamin da wani jirgin saman yakin Isra´ila ya harba ya daki motar da Hassam al-Jaabari kwamandan wata kungiyar masu kishin addinin Islama ke tafiya a ciki. To amma rahotannin baya bayan nan sun ba da sunan kwamandan da Mohammed al-Dahdouh wani dan kungiyar Jihadin Islami. Da farko dai majiyoyin asibiti sun ce mutumin dan kungiyar Hamas ne. Wata mata da ita ma ke cikin motar da wasu fararen hula 2 sun rasa rayukansu. Wata mai magana da yawun rundunar sojin Isra´ila ta tabbatar da harin makami mai linzamin amma ba ta yi karin bayani ba.