1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasɗinawa sun harba rokoki guda 3 daga zirin Gaza zuwa Isra’ila, inda ɗaya ya faɗo kusa da gidan ministan tsaron ƙasar.

Gidan rediyon Isra’ila, ya tabbatad da rahotannin cewa, wasu rokoki guda 3 da Falasɗinawa suka harba daga Zirin Gaza, sun faɗo cikin ƙasar, inda ɗaya daga cikinsu ma ya daki wani gida da ke kusa da gidan ministan tsaron ƙasar Bani Yahudun, Amir Peretz. Wata sanarwar da Hukumar sojin Isra’ilan ta bayar kuma, ta ce rokoki biyu sun daki wani gida a garin Sderot, mahaifar ministan tsaron ƙasar. Amma ta ce babu wanda ya ji rauni.

Falasɗinawan dai sun mai da martani ne ga kutsawar da dakarun Isra’ilan suka yi cikin Zirin na Gaza, inda suka harbe ’yan ta kifen Falasɗinawa guda uku har lahira.

Jaridar Haaretz ta Isra’ilan, ta buga wani rahoton da ke bayyana cewa, rundunar sojin ƙasar na shirin faɗaɗa ɗaukin da rukunanta ke yi a Zirin Gazan, don hana Falasɗinawan harba rokoki zuwa Isra’ilan.