1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Falasɗinawa sun bayyana rashin gamsuwarsu da sabon shirin ba su tallafi da rukunin nan na ’yan huɗu ya gabatar.

June 18, 2006
https://p.dw.com/p/ButM

Al’umman Falasɗinu, na ɗari-ɗari, wajen bayyana gamsuwarsu da shirin ba su tallafi na ƙasa da ƙasa da aka gabatar musu. Za miƙa tallafin, wanda rukunin da ya ƙunshi Amirka, da Ƙungiyar Haɗin Kan Turai, da Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Rasha, ya amince da shi ne ga Falasɗinawan ba tare da ya bi kan gwamnatin Ƙungiyar Hamas da suka zaɓa ba. Ƙarƙashin shirin da rukunin ɓangarori hudun ya gabatar dai, tun farkon watan Yuli mai zuwa ne za a tura kuɗi zuwa yankunan Falasɗinawan, don kula da harkokin kiwon lafiya da biyan albashin ma’aikata, kai tsaye. Duk da wannan sassaucin, ba za a soke takunkumin da aka sanya wa ƙungiyar Hamas ɗin ba, wadda ta hau karagar mulki, bayan ta lashe zaɓen Falasɗinawan da aka gudanar a cikin watan Maris da ya gabata.

Shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas, ya yi marhabin da shirin na wucin gadi, amma ya kuma ce bai wadatar ba. Tun fiye da watanni 3 ke nan dai da ma’aikatan hukumar Falasɗinawan, kimanin dubu ɗari da 65, ba su sami albashinsu ba, saboda wannan takunkumin.