Yaki da ta'addanci a yankin Sahel
May 13, 2018Talla
Ministan harkokin tsaro na Nijar Kalla Moutari ne ya sanar da hakan bayan wani zama da suka yi da takwarorinsa na sauran kasashen a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso a wannan Lahadin. Rundunar da ta kunshi dakaru dubu biyar za ta yi aiki hannu da hannu da sojin Faransa da kuma na Majalisar Dinkin Duniya da aka jibge a yankin don tunkara da kuma ganin bayan kungiyoyi da ke wa zaman lafiya a yankin barazana.