1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafutukar kare matasa daga tsattsauran ra'ayi

April 14, 2009

Haramta ƙungiyoyi masu tsananin kishin kasa

https://p.dw.com/p/HWqZ
Wolfgang SchaeubleHoto: AP

Gwamnatin Tarayyar jamus na cigaba da kokarin ganin cewar da kakkaɓe ƙungiyoyi masu tsananin ra'ayin kishi, waɗanda mafi yawa daga cikinsu ƙungiyoyi ne da suka kunshi matasa .

Ɗaya daga cikin waɗannan ƙungiyoyi dai itace ƙungiyar matasa dake kiran kansu masu kishin ƙasarsu ko kuma HDJ a takaice. Duk dacewar tana ikirarin kare muhalli da da al'umma a mazaunin kishin ƙasa, ƙungiyar nada sansanonin horarwa da matasa na soji, inda kuma anan ne ake horarsu akidoji irin na nuna wariya kamar na 'Yaan Nazi.

A yanzu haka dai tuni gwamnati ta haramta wannan kungiyar da ayyukanta. Ulrike mai shekaru 18 da haihuwa a yau ta kasance daya daga cikin 'yan wannan haramtacciyyar kungiya. Acewarta ta hanyar iyayenta ne iyayenta ne da samu shiga wannan kungiya ta HDJ......

"Da sassafe ake tashi, bayan nan akwai irin wisir da ake hurawa, sa'annan kowa yaje filin horo na karkashin ƙasa daban-daban, inda kuma anan zamu rika harin junan mu ko kuma kaiwa juna farmaki"

Akwai cibiyoyin ili masu yawan gaske inda ake cigaba da bada horarwa kan akodojin wariya kamar na zamanin Hitler. Alal misali a yankin gabashin jihar lower Saxony dake nan tarayyar jamus. Annan ma horarwar guda ce a irin wadannan ciboyi na matasa, kamar yadda tshohuwar 'yar ƙungiyar Sabine tayi bayani...

"Sun kasance mutane ne 'yan ƙasa masu ilimi, waɗanda keda akidojin kishin ƙasa, suna bada horo iri-iri da suka haɗa da na soji, kuma dole ka koyi machin irin ta sojoji da dai sauransu. Wani abu dake da akwai shine akan shirya gwaji akan dukkan horo ko koyarwa da akayi. Akan nuwa yara Nazi iri iri da tarihin kowannensu, wanda ya faro daga Adolf Hitler, da Rudolf Hess da makamantansu. Wake da alhakin fara yakin. Babu shakka ba Jamusawa bane da dai sauransu..."

Wannan ƙungiya da gwamnatin jamus ta haranta ayyukanta dai nada wakilanta matasa 400.Kazalika Saboda irin ayyuka da take tafiyarwa ,wannan kungiya ta HDJ ta faɗaɗa ayyukanta zuwa sassa daban- daban.Kamar yadda Gerhard Bücker na jihar Lower Saxony yayi nuni dashi...

"Harkokin ƙungiyar HDJ ya shafi yara kanana, waɗanda shekarunsu suka kama daga 8-14. Hakan na nufin ayayinda suke girma zasu taso ne da irin waɗannan akidoji da ake koya musu. Wannan kuwa babbar barazana ce"

A yanzu haka dai gwamnatin tarayyar jamus na cigaba da ɗaukar matakai na haramta ire iren waɗannan ƙungiyoyi masu tsananin kishin ƙasa, saboda irin tasiri da suke dashi cikin harkokin siyasar ƙasar. Ministan harkokin cikin gida na Jamus Wolfgang Schauble yayi alkawarin samarwa da yara da matasa kariya daga irin waɗannan ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi na kishin ƙasa.


Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita: Yahouza Sadissou Madobi