1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin ceto rayuwar zabiya a Senegal

Landais, Emmanuelle, Gazali Abdou Tasawa, LMJMay 4, 2016

Kadaici da rashin aikin yi da wajen kwana dama sankarar fatar jiki na daga cikin muhimman matsalolin da ke addabar al'ummar zabiya.

https://p.dw.com/p/1IiNa
Zabiya iyalan Amadu Diallo a Senegal
Zabiya iyalan Amadu Diallo a SenegalHoto: Emmanuelle Landais

A kan haka ne a Senegal kungiyar zabiya ta kasar ta yi kira da a dauki matakan gina kamfanin samar da man shafawa na maganin rana domin ba su damar samun magani cikin sauki. Daukar wadannan matakai na iya taimakawa ga kare zabiya kimanin 10,000 daga matsalar rana da sauran cututtukan fatar jiki. A Guediawaye wata unguwa da ke kewayen Dakar babban birnin kasar ta Senegal, Amadu Diallo da matarsa na da 'yaya biya kuma hudu daga cikinsu zabiya ne. Mamadou Diallo mai kimanin shekaru 13 da haihuwa shi ne yayan wadannan yara ya bayyana irin kalubalen da yake fuskanta a makaranta a matsayinsu na zabiya:

Ya ce: "Suna da kirki amma wasu lokutan ba su da shi. Ina ce masu lalle ni zabiya ne amma nima mutum ne kamar ku. Zabiya mutum ne da ke da matsalar fatar jiki kuma nufin Allah ne. A wasu lokuta kuma a makaranta ba na iya karanta rubutu a kan Allo."

Amadou mahaifin Diallo ya ce yaransa ba sa fuskantar kyama kamar yadda zabiya ke fuskanta a wasu kasashen Afirka, amma kula da lafiyarsu abu ne mai tsananin wahala. Mahamadou Bamba Diop shi ne shugaban kungiyar Zabiya ta kasa a Senegal din, ya kuma yi kira ga gwmnati da ta taimaka musu da matakan kare kansu daga rana domin inganta lafiyarsu da ma rayuwarsu. Kawo yanzu dai akwai sama da zabiya 10,000 a Senegal, wadanda gwamnatin kasar ta saka a jerin nakasassu da ke karkashin kulawar ofishin minista mai kula da mata da iyali da kuma kananan yara. Sai dai babu wani kaso na kudi da ake yi wa iyalan zabiyar kasar tanadi daga cikin kasafin kudin kasar na ko wacce shekara.