1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafutukar hamɓarar da gwamnatin Thailand

Magoya bayan Thaksin Shinawatra na bayar da jininsu domin tumɓuke gwamnatin ƙasar Thailand mai ci yanzu.

default

Jerin gwanon 'yan adawa a Thailand.

Masu zanga - zangar nuna adawa da gwamnatin ƙasar Thailand, suna ci gaba da yin jerin gwano a Bangkok, babban birnin ƙasar, inda a wannan karon, suke bayar da gudummuwar jininsu, domin zubar dashi a hanyoyin shigowa ofisoshin hukumomin ƙasar - a fafutukar da suke yi ta neman gwamnatin ta amsa kiran da suka yi na gudanar da sabbin zaɓuka - a yanzu.  'Yan adawar dai, na son samar da jinin da yawansa yakai Lita 1,000 ne, wanda suke shirin zubawa a babbar ƙofar shigowa gidan gwamnatin ƙasar da misalin ƙarfe 6 na yamma - agogon ƙasar, wato 11 na dare kenan agogon GMT . Masu jerin gwanon, waɗanda kuma aka sani da ma'abota ja'ja'yen riguna, magoyon bayan tsohon Frime Ministan ƙasar Thaksin Shinawatra ne wanda aka hamɓarar da shi a wani juyin mulkin shekara ta 2006. Suna zargin cewar, gwamnatin bata bi doka ba wajen ɗarewa kan mulki, saboda hakane - a cewarsu, ta sauka daga mulki kuma ta kira sabon zaɓe, ba tare da wani ɓata lokaci ba.  Fiye da mutane dubu 100 ne dai ke halartar zanga zangar a babban birnin ƙasar ta Thailand, wadda suka faro tun a ranar jumma'ar data gabata, kuma suka nemi Frime Ministan ƙasar dake mulki yanzu Abhisit Vejjajiva da ya rusa majalisar dokokin ƙasar.

A jawabin da Frime Ministan ya yi ta gidajen rediyo da telebijin, ya bayyana cewar, gwamnati ba zata iya biyan bukatun masu zanga-zangar ba a yanzu, domin kuwa waɗanda basu shiga cikinta ba ma suna alhakin gwamnati ta mutunta ra'ayinsu. Ya ƙara da cewar, za'a rusa majalisar dokoki ne kawai - idan har matakin zai kawowa ƙasar ci gaba.

A halin da ake ci kuma, wani jami'i a majalisar dokokin ƙasar, ya bayar da sanarwar ɗage zaman majalisar - a yau talata, kasancewar da dama daga cikin mambobin majalisar basu halarci zama ba, domin kare lafiyarsu.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Yahouza Sadisou