1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma ya yi kira ga shugabannin duniya

Babban limamin Cocin Katolika na duniya Fafaroma Françis, ya yi kira ga shugabannin duniya kan batun taimakawa matalauta da mutunta dan Adam.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Fafaroma, cikin ziyararsa a Amirka ta Kudu, ya ke amfani da wannan dama domin yin iri-irin wannan kira ga shugabannin duniya tare da yin allah wadai da tsarin jari hujja, da kuma tsarin siyasar hallaka rayukan al'umma ta dalilin son kai da abun duniya.

Fafaroman dai ya isar da jawabin jan hankali ga shugabannin kan yadda suke tafiyar da mulkinsu tare da rashin nuna tausayi ga matalauta, ta hanyar ciyar da su, da batun baiwa yara kanana damar samun ilimi, da kula da lafiyarsu, inda ya ce yin hakan na da babban mahimmanci ga mutuncin dan Adam.