1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma ya kammala ziyarar sa a Turkiyya

December 1, 2006
https://p.dw.com/p/BuZV

Shugaban darikar katolika na duniya, Fafaroma Benedict na 16, ya kare ziyarar sa ta kwanaki hudu a Turkiyya, tare da halartar taron mabiya addinin Roman Catholic.

A lokacin taron daya gudana a birnin Istanbul, Fafaroma ya jagoranci taron addu´oi da akayi.

Kafin dai fara taron, Fafaroma Benedict na , ya saki wasu fararen tattabaru guda hudu izuwa sama, wanda hakan alama ce dake nuni da zaman lafiya.

A cikin jawabin sa ga dubbannin mutane, fafaroma Benedict, ya jaddada matakin da fadar Vatikan ta dauka, na martaba hakkin bil adama a hannu daya kuma da jan hankalin mabiya addinin na Kirista.