Fafaroma ya jaddada muhimmancin ziyarar sa a Turkiyya
December 3, 2006Talla
Shugaban darikar katolika na duniya, Fafaroma Benedict na 16 ,yace akwai kyakkyawan fatan cewa ziyarar sa izuwa Turkiyya, kwalliya ta kusan biyan kudin sabulu.
Fafaroma , wanda ya fadi hakan yau, ya kara da cewa ziyarar tasa izuwa Turkiyya, na´a matsayin gada ce na ci gaba da samun kyakkyawar fahimta a tsakanin Musulmai da kuma Kiristoci.
Shugaban darikar Katolikan, wanda ya shafe kwanaki hudu a kasar ta Turkiyya, ya tabbatar da cewa ziyara ce da ba zai taba mantawa da ita ba a rayuwar sa.
A lokacin ziyarar, Fafaroma Benedict na 16, yace ya samu damar ganawa da bangarori na mabiya addinai daban daban, tare da kai ziyara izuwa wasu mahimman gurare.