Fafaroma ya bukaci kawo karshen rikicin yakin Iraq | Labarai | DW | 09.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma ya bukaci kawo karshen rikicin yakin Iraq

Shugaban darikar katolika na duniya Fafaroma Benedict na 16 ya bayyana takaici, game da halin da kasashen Iraqi da kuma wasu kasashe na Africa ke ciki.

Babban abin takaici a cewar Fafaroma, shine na yadda h.li na kashe kashen rayuka da tashe tashen hankali ya zamo ruwan dare a kasar Iraqi.

Fafaroma ya bayyana hakan ne a cikin jawabin sa na Sallar Easter,

daya gabatar a gaban dubbannin mabiya darikar ta Katolika, a dandalin St Peters dake birnin Rom.

Jawabin na Fafaroma daya gabatar a cikin harsuna 62,yace akwai bukatar daukar kwararan matakai na kawo karshen ayyukan ta´addanci da kuma yunwa dake barazana ga wasu kasashe a duniya.

Shugaban darikar ta Katolika ya kara da cewa abin takaici ne ace bil adama na gudanar da ayyukan ta´addanci da sunan addini.