Fafaroma: Afuwa ita ce zaman lafiyar Kwalambiya | Labarai | DW | 08.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fafaroma: Afuwa ita ce zaman lafiyar Kwalambiya

Fafaroma da yake jawabi ga dubban magoya bayan darikarsa a birnin Villavicencio da ke tsakiyar kasar ta Kwalambiya ya ce duk wani kokari na sulhu zai iya rushewa idan ba a yiwa juna afuwa ba.

Fafaroma Francis ya yi gargadi a ranar Juma'an nan cewa kokari da aka yi na samar da zaman lafiya na din-din-din a kasar Kwalambiya ba zai dore ba muddin ba a sulhunta ba da mutanen da aka ci zarafinsu tsawon gwamman shekaru.

Fafaroma da yake jawabi ga dubban magoya bayan darikarsa a birnin Villavicencio da ke tsakiyar kasar ta Kwalambiya ya ce duk wani kokari na sulhu zai iya rushewa idan ba a yiwa juna afuwa ba.

Blanca Real, daya ce daga cikin wadanda suka fiskanci gallazawa daga 'yan tawayen an FARC ta yi sharhi kan kiran na Fafaroma:

"Tabbas dole ne a yi yafiya domin idan kana tuna abin da aka yi maka ranka zai baci, kuma zai wahala ka cire daga zuciyarka amma muddin ka cire daga zuciya da afuwa zaka samu sauki ka rayu cikin kwanciyar hankali."