FADAR GWAMNATIN AMURKA TA YIWA DAMAR KAMA YAN TAADDA RIKON SAKAINAR KASHI.. | Siyasa | DW | 10.08.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

FADAR GWAMNATIN AMURKA TA YIWA DAMAR KAMA YAN TAADDA RIKON SAKAINAR KASHI..

Amurka tayi garaje wajen tseguntawa yan jarida wani jigo na Al qaeda data cafke a watan Yulin daya gabata.

Muhimmancin naura mai kwakwalwa wajen halakan yan taadda.

Muhimmancin naura mai kwakwalwa wajen halakan yan taadda.

Akwai alamun cewa hannun agogo ya koma baya,a dangane da kokarin daya dauki gwamnatin Bush shekaru 3 na farautar yan kungiyar Al Qaeda,bayan bayyana sirrin wani babban jigo dake da halaka da kungiyar yan taaddan.

Mai shekaru 25 da haihuwa kuma wanda ya shaha cikin harkoki na naura mai aiki da kwakwalwa watau Komfuter,Mohammed Naeem Noor Khan,ya jima yana bada hadin kai wa yansandan Pakistan da cibiyar Leken Asiri ta Cia ta Amurka,tun bayan cafkeshi da akayi a asirce a Lahore ranar 12 ga watan yuli,kafin jaridar New york Times ta wallafa sunansa ranar talatar data gabata,bayan samun hiran tushen batun da fadar gwamnati ta White house.

Gwamnatin Bush wadda ta dauki tsarara matakan tsaro dangane da shirin barazanar kaiwa jihohinta 3 hare hare,baya samun labari daga Khan,ta gudanar da wannan taron manema labaru domin kwantar da hankalin jamaa daga razana daga barazanar kai wannan hari,musamman ma bayan ance akasarin bayanan kai harin shekaru da dama da suka gabata aka shiryasu.

Hukumomin leken asirin Pakistan da Britania,kamar yadda rahotanni sukayi nuni dashi sun bayyana takayyacinsu dangane da wannan liki da aka samu,wanda ya sanya yansandan birtania suka gaggauta cafke wasu da ake zargi da kasancewa yan alqaeda,su 13,wadanda kuma ke halaka ta yanar gizo gizo da Mr Khan.Ayayinda wasu guda biyar da ake nema ruwa a jallo suka tsere.

Bayyana Khan,mutumin dake zama babban nasara da Amurka ta tabayi na cafke wani jigon kungiyar Alqaeda,na mai zama babban asara a bangarenta,tare da koma baya a kokarin da takeyi na ganin bayan kungiyar da shugabanninta.,ata bakin juan Cole,masani kann harkokin da suka shafi yankin gabas ta tsakiya dake jamiar Michigan.

A hannu guda kuma,Amurka na neman biyu daga cikin wadanda Britanian ta cafke watau,Abu Issa al Hindi da Babar Ahmed.Amurkan dai na zargin Ahmed da leken asiri kann jirgin sojin ruwa na kasar,wanda ake kira Constellation,a shekarata 2001,wanda watanni shida bayan harin Alqaeda ne wa Amurkan,aka kai wani a Yemen.Ayayinda Hindi anashi bangaren ,ake zargin tura shi leken asirin wasu masanaantun kudade na Amurka dake biranen New York da New Jesey da Washinton DC,wanda kwanaki 8 bayan nan ne aka sanar da barazanar yan ta kifen.Bincike dai yayi nuni dacewa wani File da aka samu a gaban Komfutan Hindi ya kunshi bayanan shirin kai hare hare wa wasu masanaantun kudi da suka hadar da Bankin duniya,da IMF,a birnin Washinton.An dai bayyana cewa shekaru 3 kenan da akayi shirin kai wadannan hare hare,tare da wasu batutuwa na sirri da suka hadar da bayanan Khan,kafin Fadar White house ta mayar da hannun agogo baya.

Mai bawa shugaba Bush shawara kann harkokin tsaron kasa,Condoleeza Rice ta tabbatar da wannan hira da akayi da manema labaru a yayinda da take amsa tambayoyi daga CNN.

Hukumomin pakistan,sun bayyana bacin ransu kann wannan batu musamman dangane da irin matsin lamba da suke fuskanta daga Washinton,inji ministan cikin gida Faisal Saleh Hayyat.

Shi kuwa tsohon babban mai gabatar da kara na SASHIN Sharian Amurka John Loftus,cewa yayi ba karamin asara gwamnatin Bush tayi ba na bayyana wannan talikin Khan,wanda da hakane zaa iya gano inda jiga jigan kungiyar Alqaedan suke da yadda suke tafi da harkokinsu.

Zainab Mohammed.