1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fadan yan tawaye ya sake barkewa a jamhuriyar democradiyar Congo--

Jamilu SaniJune 2, 2004

Tun bayan barkewar fadan yan tawaye a garin Bakuva na gabashin jamhuriyar democradiyar Congo,majalisar dikin duniya ta ce zata aika dakarunta na kiyaye zaman lafiya wanan birni----

https://p.dw.com/p/BvjD
Barkewar fadan yan tawaye a Congo
Barkewar fadan yan tawaye a CongoHoto: AP

A jahuriyar democradiyar Congo sanarwar data fito daga wani kanal din kungiyar yan tawayen kasar a yau laraba,ta baiyana cewa yan tawaye sun kwace garin Bakuva daga hanun dakarun gwamnatin Congo,cikin dauki ba dadin da suka yi da juna wanda kuma aka baiyana da cewa na bazarana ga yarjejeniyar zaman lafiyar jamhuriyar ta democradiyar Congo.

Koda yake yan tawaye sun bada sanarwar cewa sun kwace garin Bakuva daga hanun dakarun gwamnatin Congo,to amman kuma wani jami’in majalisar dikin duniya dake garin na Bakuva,ya furta cewar har yanzu dakarun gwamnatin Kinshasa ne ke rike da wanan birnin na gabashin Congo mai tsaunuka da ya hada kann iyaka da kasar Rwanda.

A makon da ya gabata ne dai dakarun gwamnatin Congo suka fatata da mayakan madugun yan tawaye kanal Jules Mutebutsi,a kokarin da suka yi na hana su rike ragamar mulkin garin Bakuva.

Madugun yan tawaye Mutebutsi ya shaidawa kamfanin dilancin labaru na Reuters cewar,sune ke rike da ragamar mulkin birnin na Bakuva na gabashin jamuhuriyar ta democradiyar Congo.

Bugu da kari madugun yan tawayen na Congo,ya kara da cewar,abinda ya rage musu shine,su cigaba da fafatar sauran dakarun gwamnatin Congo da suka rage a garin na Bakuva,inda yace a halin yanzu yan tawaye zasu cigaba yaki da dakarun gwamnatin Congo da suka boye a kann tsaunuka har sai sun kore su daga wanan birnin baki daya.

Mai magana da yawun majalisar dikin duniya a Congo,ya baiyana cewar ba ko kanshin gaskiya cikin irin kalaman dake fitowa da madugun yan tawaye Mutebutsi dake nuna cewar sune ke rike da garin Bakuva.

Kakakin na majalisar dikin duniya a jamhuriyar democradiyar Congo,ya baiyana cewar,dakarun gwamnatin Congo ke rike da garin na Bakuva,kuma a halin da ake ciki sun an aika dakarun na gwamnati kann titunan birnin na Bakuva,da nufin fatatakar mutanen da suka shiga wasosan kayan jama’a.

An dai baiyana cewar sabon fadan da ya barke a garin Bakuva ,wanda kuma aka yi asarar rayuka da dama a cikinsa,ya kasara dukanin yarjejeniyar da aka cimma ta zaman lafiyar Congo,duk kuwa da kokarin da gwamnatin hadin kann kasa ta sanya a gaba na tabatar da ganin an sami dorewar zaman lafiyar Congo.

Wani wanda ya ganewa idonsa abinda ke faruwa,ya baiyana cewar ya ga lokacin da mutane ke wasosan kayan jama’a a birnin na Bakuva,yayin kuma da sanarwar kungiyar Red Cross ta Congo ta baiyana cewa mutane 39 suka kwanta dama,wasu kuma 82 suka sami raunuka tun lokacin da fadan yan tawaye ya barke a barin Bakuva na gabashin jamhuriyar democradiyar Congo ranar larabar data gabata.