FADADA WAADIN GABATAR DA KOKEN ZABEN SHUGABAN KASA A AFGANISTAN. | Siyasa | DW | 13.10.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

FADADA WAADIN GABATAR DA KOKEN ZABEN SHUGABAN KASA A AFGANISTAN.

Shugaban riko kuma Dan takara,hamid Karzai.

Shugaban riko kuma Dan takara,hamid Karzai.

Jamian kula da harkokin zabe sun sake fadada waadin gurfanar da koke koken yan takara a zaben shugaban kasa daya gudana a Afganistan ranar asabar zuwa gobe Alhamis.

Jamian kula da harkokin zaben na Afganistan sun bayyana cewa sun zartar da kara waadin da saoi 48 domin bawa yan takaran damarv gabatar da cikakkun takardunsu na koke koken.Kakakin hukumar binciken harkokin zaben na kasa da kasa da MDD ta nada Graig Jenness,ya fadawa taron manema labaru cewa yanzu haka suna da takardun koke 43,ya zuwa waadin jiya da yamma da aka bayar.

Shugaba Hamid Karzai na Afganistan din na daga cikin yan takara 4 da suka gabatar da koraffinsu a gaban wannan komiti.Ana kyautata zaton Hukumar zaben hadin gwiwa ta kasar da wannan komiti na Kwararru na kasa da kasa mai wakilai 3 da MDD ta nada,zasuyi kwakkwarar bincike kann zargin magudi da aka tabaka a zaben na ranar Asabar data gabata.

Kafa wannan kwamiti na kwararrau zai taimaka matuka gaya wajen warware rikicin dake neman yin barazana wa zaben wannan kasa dake tsakiyar Asia,zaben dake zama zakaran gwajin dafin Democradiyya a karon farko a wannan kasa,kuma dukkan yan takaran sunce zasu amince da sakamakon binciken wannan hukuma ta hadin gwiwa.

Banda Dan takaran Amurka kuma shugaban riko na Afganistan din Hamid Karzai,wanda kuma ake sa zato shine zakaran wannan zabe,Babban abokin kalubalensa Yunus Qanooni ya gurfanar da nashi koke,shima shugaban kabilar Hazara Mohammed Mohaqeq,kazalika Ghulam Farooq Nijrabi ,sun gurfanar da kararrakinsu kann wannan zabe.Sai dai baa sanar da irin abunda ke kunshe cikin kararraki da suka gabatar ba.Sai dai daya daga cikin koken da aka gabatar shine,ruwan Inki na dangwalan yatsa da akayi amfani dashi ranar zaben na iya wankewa,idan aka zuba masa ruwa.

Ayayinda ake ta wannan Commandan rundunar Amurka dake Afganistan Liuetenant General David Barno,ya fasdawa manema labaru cewa zaben shugaban na Afganistan na mai nuni da yadda aka shawo kann matsalar taaddanci a wannan kasa.Yace ana iya danganta hakan ne da yadda miliyoyin yan kasar sukayi dafifi zuwa cibiyoyin zabe ranar asabar domin kada kuriunsu,yace wannan kadai ya isa ya tabbatar dacewa an samu nasaran yaki da ayyukan tarzoma a wannan kasa,sabanin yadda ake hangen tashin hankali lokacin zaben.Duk dacewa an fuskanci hare haren daya bar yansanda 8 da fararen 3 mace gabannin zaben,babu wani rahoto dangane da hari a kowanne daga cibiyoyin zaben daya gudana.

Shi kuwa sakataren harkokin waje na Amurka Colin Powel cewa yayi ,hakan ya hakikance cewa Democradiyya na iya samun gindin zama a kasar Iraki,domin alummar Afganistan tayi nuni dacewa Democradiyya zata iya tabbata a koina a duniya,idan har aka bata dama.

Zainab Mohammed.