Fadada kungiyar Eu zuwa 27 | Labarai | DW | 31.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fadada kungiyar Eu zuwa 27

Saoi kalilan ne ya ragewa kungiyar gammayar Turai ta dada fadada da karin kasashe biyu,wanmda zai kawo ga sadadin wakilanta 27.Kasashen Romania da Bulgaria zasu hade da kungiyar ta Eu a hukumance bayan karfe 12 na daren yau,wanda ke nufin sabuwar shekarata 2007 ,idan Allah ya kaimu.Wannan bukin shigar da waddanan kasashe biyu cikin kungiyar yazo daidai da lokacinda da Jamus zata karbi zagayen shugabancin kungiya daga kasar Finland,na tsawon watannim shioda masu gabatowa.Ministan harkokin wajen jamus Frank-Walter Steinmeier ,zai ziyarci biranen Bucharest da Sofia ,domin halartan bukin shigar da sabbin kasashen biyu cikin EU.