1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

FADADA AYYUKAN SOJOJIN JAMUS A AFGANISTAN.

September 30, 2004

Karuwan tashe tashen hankula gabannin zabe.

https://p.dw.com/p/Bvg4
Sojojin Jamus a Afganistan.
Sojojin Jamus a Afganistan.Hoto: AP

A yau ne dukkan yan majalisar Dokokin nan Jamus suka cimma yarjejeniya na marawa gwamnatin kasar baya,a dangane fadada ayyukan sojojin kiyaye zaman lafiyarta dake Afganistan da karin watanni 12.

An cimma wannan yarjejeniya ne ta hanyar kada kuriu,duk da harin Rokoki da aka kaiwa sansanin sojin Jamus din dake ayyukan kiyaye zaman lafiya a Arewacin Afganistan jiya Laraba,harin daya raunana Sojin Jamus din 3 dana kasar Swiss guda 2.

A yanzu akwai kimanin Dakarun Jamus 2,000 daga cikin kimanin sojoji 7,000 dake ayyukan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa,a Afganistan din,wadanda kuma ke zama mafi yawan irin wannan ayari daga kasa guda.

Sojojin Amurka dubu 16 da 500 na yaki da mayakan sari ka noke a kudancin kasar.

Ayayin kada wannan kuria yau a majalisar ta Jamus,yan majalisa 509 suka amince da bukatun na gwamnati,48 sukayi adawa,kana 3 suka ki bayyana a zaman majalisar.

A yanzu haka dai waadin Sojin Jamus din na karewa ne ranar 13 ga Oktoba,yini 4 bayan zaben shugaban Afganistan ,zaben da kungiyar Al qaeda da Burbudin rusasshiyar gwamnatin Taliban suka lashi takobin cewa bazai gudana cikin kwanciyan lafiya ba.

Ministan harkokin waje Joschker Fischer yayi kira ga da kakkausar murya wa yan majalisar dasu amince da karawa sojin kasar lokacin ayyukansu a wannan kasa dake fuskantar barazanar yan sakai,inda yace gwamnati bata zabin daya wuce hakan ayanzu da ake kokarin mayar da Afganistan din zaunanniyar kasar Democradiyya.

Shi kuwa ministan tsaro Peter Struck cewa yayi,harin da aka afkawa Jamusawan dashi a Afganistan na dada tabbatar dacewa akwai bukatar matsa kaimi kann matakan tsaro a dai dai wannan lokaci da ake ciki,na sabunta democradiyyar kasar.

Jamusawan da aka kaiwa hari a jiyan dai na bangarenayarin masu kula da ayyukan sake ginin kasar a garin Kunduz,wanda ke zama daya daga cikin biyun da Jamus ke daukan nauyi a Arewacin Afganistan.Ayanzu haka dai an dauki matakai tsaurara na tsaro a wannan sansanin dake da Sojoji 270,da fararen hula 30,sauran ayarin sojoji 110 na garin Faizabad,ayayinda mafi yawan saran Sojin Jamus din ke babban birnin Kasar watau Kabul.

Jammiyyar shugaba Gehard Schroder ta SPD,da the Greens dake kawance da ita,da kuma mai adawa ta CDU ,sun amince da fadada ayyukan dakarun jamus din da karin watanni 12,Ayayinda FDP da PDS suka nuna adawarsu.

Kasashe 30 suka bada gudummowan sojin kiyaye zaman Lafiyan na Afganistan a karkashin tutan MDD a watan Disamban shekarata 2001,bayan an kifar da gwamnatin yan Taliban.